Gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta daga wani labara dake yawo cewa gwamnatin jihar yanzu haka na biyan ma’aikatan jihar bashin albashin watanni 6 (shida) da suke bi ta, ta hanyar amfani da makudan kudade na tsohuwar naira da aka haramta ci gaba da amfani dasu.
Cikin wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun, mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai a Zamfara Ibrahim Dosara.
KU KARANTA: Abokan Adawar Tinubu Tuni Sun Mallaki makudan kudade a hannun su – El-rufai
A cewar gwamnatin Zamfara wannan labara farfaganda ce kawai da wasu masu marasa kishin jihar ke kokarin yadawa, domin bata sunan Gwamna, saboda hassadar da suke yi ga dimbin nasarorin da gwamnatin jihar Zamfara ta samu a karkashin jagorancin mai Bello Mohammed Matawallen Maradun, a cikin shekaru uku da rabi na mulkin sa da kuma goyon bayan da gwamnatin ke samu daga kowane lungu da sako na jihar Zamfara kan zaben da ke tafe.
A don haka gwamnatin ke shawartar jama’a da su yi watsi da irin wannan rashin fahimta da yaudara, domin ba shi da tushe balle makama.
Jama’a sun kwana da sanin cewa Gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun bai taba tsallake wata guda ba tare da biyan albashin ma’aikatansa ba tun daga lokacin gwamnatinsa zuwa yau.
Ma’aikatan jihar da kungiyar kwadago su ne shaida kan hakan, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A kwanakin baya, gwamnatin Zamfara ta kuma aiwatar da mafi karancin albashin ma’aikatan jihar 30,000 kuma tun a watan Nuwamba suke cin gajiyar mafi karancin albashin.
Wannan duk na zuwa ne bayan da kuma gwamnatin ta rabar da gidaje sama da 1000 akan rangwamen kashi 40 ga ma’aikata da nufin tabbatar da cewa kowane ma’aikaci ya mallaki gidan kansa bayan ya yi ritaya daga aiki.
An kuma baiwa ma’aikatan damar biyan kashi sittin cikin dari cikin shekaru goma, duka a kokarin gwamnatin na ganin kowanne dan jihar ya dara.
A karshe yayi fatan masu hali irin wannan zasu daina tare da kokarin tabbatar da gaskiya, maimakon yada karya don cimma bukatun wasu.
A wani labarin kuma: Ba don Tinubu ya faɗi yasa suka canja Naira ba, suna shirin sanya mulkin soja – El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa mutanen da ke yakar jam’iyyar All Progressives Congress, APC da dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ne suka ɓullo da shirin.
Shugaban na Kaduna ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Alhamis.