Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a ranar Alhamis ya kaddamar da shirin gina Otel mai daraja ta uku wanda zai lashe zunzurun kudi har naira biliyan tara. Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya labarto cewa; Otel din za a gina shi ne a karkashin hadin guiwar wani kamfani mai zaman kansa mai suna Finesse and Estetics Nigeria Limited da kuma gwamnati jihar.
Da yake bayani a wurin taron wanda ya gudana daura da Babbar Sakatariyar gwamnati dake Gusau, gwamnan ya ce wannan aikin yana daya daga cikin ayyukan da ya yiwa al’ummar jihar alkawarin ganin an yi shi ne a yayin jawabin kaddamar da shi a karagar mulki.
Ya ce ya yi alkawarin samar da yanayin da za a samu masu zuba hannun jari daga kasashe daban-daban da kuma nan cikin gida a jihar domin samar da guraben ayyukan yi ga al’umma daban-daban.
Ya tabbatar da cewa; wannan aiki idan aka kammala shi, mutane 3, 000 ne za su samu aikin yi, sannan a cewarsa shi kansa ginin Otel din zai bai wa masu zuba hannun jari a jihar wata damar samun wurin sauka a duk lokacin da suka kasance a jihar.
Har wala yau ya ce sakamakon rashin kyakkyawan wurin sauka, ya sanya jihar ba ta samun ana shirya manyan taruka na duniya, tarukan horaswa da dai sauran su. Ya ce; ko wannan dalilin ma abin a gina Otel din ne. Ya ce Otel din mai suna ‘The 100 Keys Paradise Hotel,’ wanda kamfanin Amber Hospitality Services Limited zai lura da shi, ana sa ran kammala shi cikin wata 30.