Shugaban Hukumar kula da ilimin Firamare a Nijeriya Dakta Hameed Boboyi ya ce yanzu haka asusun ajiyar hukumarsa na da kudin da ya wuce naira biliyan 41 da aka ware domin amfani da su wajen inganta makarantun Firamare a fadin kasar amma gwamnatocin jihohi sun kasa zuwa su karba.
Yayin da yake jawabi ga kwamitin ilimi na Majalisar Dattawa, Boboyi ya ce tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020 Jihohin kasar da Abuja sun karbi naira biliyan 143 daga cikin naira biliyan 184 dake asusun hukumar.
Sai dai jami’in ya zargi Jihohin da gazawa wajen zuwa su karbi wadannan kudade wadanda aka gindaya sharudan karbar su da suka hada da gabatar da ayyukan da ake bukatar yi da kason kudin da jihohin za su bayar kafin ita gwamnatin tarayya ta hannun hukumar ta bada na ta kason.
Shugaban hukumar ya ce babu wata Jiha a Nijeriya da ta karbi kudi daga hukumar a shekarar da ta gabata, yayin da Jihar Ogun ta gaza wajen karbar na ta kudaden a shekarar 2018, sai kuma wasu jihohi 10 da suka kasa karbar nasu kason a shekarar 2019.
Wadannan jihohi sun hada da Kebbi da Niger da Ogun da Enugu da Anambra da Ebonyi da Imo da Edo da Abia da kuma Lagos, sai dai yace a yan kwanakin da suka gabata Jihohin Abia da Lagos da Kebbi sun zuba nasu kason.
Dr Boboyi yace jihohi 30 da Abuja sun yi nasarar aiwatar da manyan ayyukan shekarar 2018 amma banda jihohi 6 da suka hada da Anambra da Imo da Kaduna da Kwara da Ogun da kuma Plateau.
Jami’in ya ce a shekarar 2019 kuwa jihohi 8 ne suka aiwatar da nasu ayyukan, banda jihohi 28 da kuma Abuja.