Cif Afe Babalola, wanda ya kafa Jami’ar Afe Babalola dake Ado-Ekiti, ya ce gwamnonin jihohi suna kafa jami’o’i ne saboda dalilai na siyasa.
Ya ce da yawa daga cikin irin wadannan jami’o’in an same su da rashin dorewa bayan da watakila gwamnonin da suka kafasu sun bar mulki.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi a wurin taro karo na 9 da cibiyar da ta karrama gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum; Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi; Ewi na Ado Ekiti, Oba Rufus Adejugbe da Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, da digirin girmamawa.
“Abin takaicin shi ne, Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da kafa jami’a mai reshen daya mazaba”
“Mutum ya tuna irin halin da jami’o’in jihar da wasu gwamnoni suka kafa a yankunansu, wadanda ba su dawwama ba, bayan sun bar kujerar mulki.
“Ina kiran wadannan jami’o’in, a matsayin jami’o’in da aka kafasu don siyasa. Ina kira ga Kumar kula da Jami’oi NUC, wacce a doka ta ba da izinin amincewa da kafa jami’o’i, da ta tabbatar an bi sharuddan da doka ta gindaya kafin kafa jami’a”
“Hukumar NUC a shafinta na yanar gizo ta kasance tana buga sunayen jami’o’in da ba su dace ba duk shekara. Hakan na nufin ba a dauki mataki kan wadanda aka gano a shekarun baya ba.”
“Lalacewar fannin Ilimi ta sanadiyar irin da wadannan jami’o’in ba bisa ka’ida ba, ba za a iya gyarawa ba cikin kankanin lokaci,” in ji Babalola.
Ya bukaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kuma hukumar kula da jami’o’i ta kasa da su kama tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen gudanar da ayyukan jami’o’in da ba su dace ba a Najeriya.
Ya ce yakamata a yi hakan ne domin kare tsarin ilimin kasar daga durkushewa
Ya shawarci hukumar da ta dakatar da samar da abin da ya kira “cibiyoyin da basu dace ba” da ke lalata tsarin Ilimi.
Da yake jawabi a madadin wadanda aka karrama, Zulum ya dora alhakin lalacewar fannin ilimi a kan matsalar Yawaitar garkuwa da mutane da fashi da makami, da kuma kashe-kashe da ake Samu a kasar nan.