Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bada tallafin Naira miliyan hamsin ga yan uwa da iyalan wadanda hatsarin Jirgin ruwa ya ritsa da su a Jihar Kebbi.
Shugaban Kungiyar Kayode Fayemi shi ya sanar da haka yayin da ya ziyarci Jihar don isar da ta’aziyar su da kuma jaje ga al’ummar Jihar.
Gwamna Fayemi ya ce wannan al’amari da ya sanadiyyar salwantar rayukan Mutane akalla dari ba karamin al’amari bane, kuma babu makawa gwamnati za ta yi kokarin inganta bangaren bada agajin gaggawa.
“Na zo Jihar Kebbi ne a matsayina na shugaban gwamnonin Najeriya don mika ta’aziya da kuna jaje wa al’ummar Jihar bisa wannan mummunar al’amari” cewar Fayemi.
Gwamna Fayemi ya samu rakiyar gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal da kuma na Pilato Simon Bako Lalong.
Jirgin ruwan dake dauke da mutane sama da 200 wadanda galibin su mata ne, ya kife ne a kauyen Tsohuwar Labata yan kilomita zuwa masaukinsa.