• Gwamnonin APC sun amince da Karin wa’adin jagorancin kwamitin jam’iya APC.
• “Karawa Mai La Buni wa’adin zai taimaka wurin Kai jam’iyar mataki na gaba” inji masu ruwa da tsaki na jam’iyar.
•A dai ranar Juma’ar data gabata ce, jami’iyar APC ta karawa Buni wa’adin jagorancin kwamitin.
A jiya Asabar ce, Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC sun ka amince da sabon karin wa’adin da a kayi wa Mai Mala Buni, domin cigaba da jagorantar kwamitin rikon kwarya na jam’iyar.
Sun kara da cewa, karin wa’adin zai taikakawa jam’iyar wujan samun isasshen lokacin shiri, dangane da babban gaggamim da jami’iyar zata yi na kasa baki daya.
Gwamnar jihar Kebbi kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin jami’iyar Jami’iyar, Sanata Atiku Bagudu ne, ya bayyana wa mane ma labarai hakan, bayan taron da suka gudanar a daren ranar Larabar da ta gabata, inda ya yaba, da karin wa’adin da kai wa Buni, ya kuma ce, hakan zai taimaka wajan ceto jam’iyar.
Kwamitin zartarwar jam’iyar ce dai, ta bai wa Buni jagorancin jam’iyar na watanni shida, tun a watan Disambar shekarar 2020, da nufin dai-dai ta rikice-rikicen jam’iyar a baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Majalissar Wakilai ya dauki nauyin karatun Yara 38 a garin Abuja
Idan za’a iya tunawa dai, an karawa Mala Buni wa’adin jagorantar kwamitin tsare-tsaren jam’iyar ce, karo na biyu, tun a ranar Juma’ar data gabata.
Comments 1