Gwamnonin Arewa maso gabashin ƙasar nan sun yi kira ga gwamnatin tarayyar da ta ƙwace aikin daga ‘yan kwangilar da suka kasa ci gaba da ayyukansu, domin baiwa wadanda za su iya aikin cikin takaitaccen lokaci don ci gaban al’ummar yankin.
Ƙungiyar gwamnonin sun yi wannan kiran ne a wani taron gwamnonin shiyar arewa maso gabas da suka gudanar a garin Maiguduri na kwana biyu. Taron ya samu halartar Gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, shi ne ya jagoranci taron, ya kuma karanta wa manema labari jawabin ƙungiyar gwamnonin inda ya ce, sun yaba wa gwamnatin tarayya tare da rundunar sojin ƙasar nan a bisa yaƙin da suke yi da ƙungiyar tada ƙayar baya ta Boko Haram.
To sai dai sun yi kira ga sojojin da su kara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da tashe-tashen hankula.
Ƙungiyar gwamnonin ta kuma yi kira ga ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da ta tabbatar da an mai da hankali sosai wajen jan ruwan yankin tafkin Chadi wanda al’umma da yawa ke amfani dashi.
Sannan sun buƙaci da a samar wa ‘yan sanda makamai na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaƙi da ƙungiyar ta Boko Haram.
Gwamnonin sun yi alƙawarin yin aiki tare domin ci gaban al’ummarsu, musamman wajen gano ma’adanan ƙarƙashin ƙasa, kamar su Man Fetur, iskar Gas, harkokin noma da masana’antu.
Sannan sunyi alkwarin haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen haɓɓaka makarantun tsangaya da karfafa karatun Islamiyya da na zamani da kuma hana yawon barace-barace.