Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na Nijeriya, Babagana Munguno da duka gwamnonin yankin arewa maso yammacin Nijeriya bakwai na taro a Kaduna don lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A baya-bayan nan, ƴan bindiga sun addabi yankin kuma sun kashe ɗaruruwan mutane da raba wasu da muhallansu.