Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta bayyana baƙin cikin ta akan rasuwar Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba, jikan marigayi Sir Ahmadu Bello.
Danbaba ya rasu a ranar Asabar a Kaduna.
Shugaban Ƙungiyar, kuma Gwamnan Jahar Filato Simon Lalong ya yi ta’aziyya ga iyalansa da Masarautar Sokoto, da Yankin Arewa a cikin wani saƙo da Daraktan Ƴan Jarida da Hulɗa da Jama’a Dr Makut Macham ya sanyawa hannu aka fitar a ranar Lahadi a Jos.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Har yanzu bamu sanar da Shiga Yajin Aiki — Cewar ASUU
Ƙungiyar ta bayyana Magajin Garin Sokoto a matsayin Basarake da ake ganin darajar sa da yabi bayan kakan sa, tare da amfani da ikon sa wajen yiwa al’ummar sa aiki da samar masu ayyukan yi.
Ƙungiya ta kuma aika saƙon ta’aziyya ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, Gwamna Aminu Tambuwal, da Gwamnati da Al’ummar Jahar.