Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe a ranar Laraba sun ayyana dokar zaman gida a jihohinsu a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona.
Gwamna Yahaya ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yiwa ‘yan jihar ta kafafen watsa labarai, a yayin da kuma ya dakatar da dukkanin wani nau’in tarukan addini a jihar.
Sannan har wala yau an dakatar da dukkanin kasuwanni da kuma nau’ikan tarukan jama’a a fadin jihar. Tare da haramta shigowa jihar daga wata jihar, da kuma bada umurnin rufe makarantun Islamiyyu da Tsangayu.
Haka ma abin ma yake a jihar Nasarawa.