Gwamnoni biyar na yankin kudu maso kudu sun amince da goyon bayan Gwamnatocin Jahohin Rivers da Lagos, akan hana Hukumar tattara kuɗaɗen haraji karɓar haraji na VAT a gaban kotun ƙoli.
Gwamnonin sun bayyana haka a wani taro da ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Kudu suka gabatar a gidan Gwamnatin jahar dake Fatakwal, jahar Rivers a ranar Litinin.
Gwamnonin da suka halarta sun haɗa da; Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike, da Ifeanyi Okowa na jahar Delta, da Gwamnan Akwa Ibom Udom Emmanuel, da kuma Gwamnan Jahar Edo Godwin Obaseki, gami da Douye Diri na jahar Bayelsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Facebook Da Instagram Gami Da WhatsApp Sun Daina aiki
Gwamnan jahar Cross Rivers Farfesa Ben Ayade, bai samu damar halarta ba, kuma bai turo wakili a taron ba.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Kudu kuma Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa, wanda ya karanta mal’amari guda biyar da aka tattauna bayan kammala taron, yace ƙungiyar ta goyi bayan jahohi su riƙa karɓar kuɗaɗen haraji.
Haka zalika, ƙungiyar ta kuma amince da ƙirƙiro da wasu jami’an tsaro da za’a ƙaddamar nan bada jimawa ba, wanda aka yiwa laƙabi da BRACED, wanda ya samo sunan daga Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River, da Edo, da Delta.
Okowa yace “duba dacewa, jahohin suna da reshen Rundunar tsaro ta BRACED, Mun amince da ƙirƙirar jami’an tsaro na shiyya, wanda za’a ƙaddamar nan bada jimawa ba.