Wakilinmu Bala Mukhtar Maiduguri
Wasu Daruruwan ‘Yan Gudun Hijirah, a Maiduguri Babban Birnin Jihar, sun Fusata Mutuka, Inda a Yau Alhamis Suka Fito Mazan su da Mata, domin Nu na Rashin Gamsuwar su ga Halin Kunci da Yunwa, Karancin Abinci, da kuma Yadda ake ma ‘Ya’yan su Fyade da sunan Taimako, inji su.
Sun rika Fadin Kalaman Tausayawa Inda wasu ke Fadin Gwara ma a Mayar da mu Garuruwan mu Boko Haram su kashe mu da mu rika yin Mutuwar Dai-dai da Sunan ana Ba mu Agaji.
Wata Mai suna Zaliha, da Wakilinmu Bala Mukhtar ya zanta da Ita cewa ta yi kullum sai wasu sun Mutu a nan saboda yunwa, wasu yaran kuma an kallafa musu zama ‘yan iskan dole saboda su Samu Abin ci, inji ta.
Yayin da wasu daga cikin ‘yan Gudun Hijrah suka ce sam ba sa zargin kowa daga wannan halin da suke ciki illa mahukunta, a Najeriya.