Tsohuwar wacce ta Lashe Macen da tafi kowa kyau dake wakillatar kasar Amurika Cheslie Kryst ta mutu ta na da shekaru 30 a duniya.
Danginta da kuma rundunar yan sandan birnin New York sun tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta ruwaito.
A cewar yan sandan Gwarzuwar da ta taba lashe gasar Macen da ta fi kowacce kyau a kasar Amurika a shekarar 2019, Ta yi tsalle ne daga wani bene dake Manhattan kafin mutuwar ta.
A cikin sanarwar da iyalan marigayiyar suka fitar kuwa ya nuna cewa, ” Cikin Alheni da tahini hankali Muna bakin cikin sanar da Al’uma Mutuwar Abun kaunar mu Cheslie. Haskakawarta ya Sanya mutane a fadin duniya kasancewa cikin farinciki Saboda tsabar kyawunta da kuma nuna kauna.”
Sai dai kafin mutuwar ta, Tsohuwar gwarzuwar ta Amurika, ta yada hotunan ta a shafinta na Instagram dauke da rubutun “Ina Fatan wannan Rana ta kasance Mai ni’ima a gare ku”
Kryst kwararriyar Lauyace wacce ta amshi Digiri Uku a mabanbantan jami’o’i biyu, Kuma bayan kasancewarta masaniya a fannin Shari’a ta kasance Yar Kabilar Arewacin Carolina dake hada rahotannin nishadi a Tashar Extra TV
“Zukatanmu sun Karaya, domin Cheslie ba gudunmawa kawai take bayarwa a shirin mu ba,ta kasance daya daga cikin Ahalin Tashar Extra, Kuma mutuwar ta ya taba zukatan dukkannin Ma’aikatan wannan Tasha, don haka Muna Mika ta’aziyarmu ga kafatanin iyalan ta da kuma abokanta” inji Tashar Extra TV, a cikin wata sanarwa da ta fitar.