• “Zamu iya kutsawa Mekelle nan da makonni masu zuwa, idan bukatar hakan ta ta so”. Inji Redwan.
• An tsagaita wuta ne domin kai kayan agajin gaggawa.
• Shugaban Yan awaren Tigray ya bayyana matakin tsagaita wutar amastayin abun al’mara.
A yau Laraba ne Redwan Hussein Mai magana da yawun rundunar hadaka ta gwamnatin kasar Habasha, ya bayyana cewa, rundunar sojin kasar zata iya sake afkawa yankin Tigray na babban birnin Mekelle a cikin wasu makwanni idan bukatar hakan ta taso, inda ya ce, tsawaita wuta da aka ayi daga ranar Monday anyi shi ne domin kai kayan agajin kaggawa.
Kuma wannan shine karo na farko da gwamnatin Habasha, ta fito tayi wani magana tun ba yan da Dakarun Tigray suka fara kwace iko da birnin Mekelle, a cikin makon Nan.
Ya ce ” Habasha ta fuskanci wani hari daga kasar waje, sabida wani rikita-rikita,” kamar yadda Hussein ya bayyana wa wasu mane ma labarai, da ya ke Mai da martani ga kasar Sudan.
Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Litinin ce dai, Dakarun Tigray su ka kutsa wani yanki a Makelle babban birnin yankin, inda daga bisani, gwamnatin kasar, ta sanar da tsagaita wuta, da ya fara aiki a nan ta ke.
Inda a ranar Talata kuma, Mai magana da yawun al’umar na Tigray Getachew Reda ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Maganar tsawaita wutar alma’ra ce kawai. Tunda an kulle layun waya a Mekelle tun ranar Larabar data gabata,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashida Mai Sa’a ta jaddada maganar ta
A karshe kuma Redwan ya bayyana matakin a matsayin na siyasa, inda ya kuma ce, “Cikin sauki Zamu iya kusa wa Makelle cikin kasa da mako uku” inji shi.