Kasar Habasha ta sake baiwa kamfanin Jiragen sama na Boeing 737 Max damar cigaba da zirga zirga-zirga a kasar ta.
Hukumar da ke kula da sufurin jiragen Sama a kasar ce ta sanar hakan, tun bayan dakatar da Kamfanin da suka yi sanadiyar wani hadarin jirgin Kamfanin dauke da fasinjoji, bayan tashinsa daga Adis Ababa babban birnin ƙasar shekaru uku da suka gabata.
A wancan lokacin da hatsarin ya faru dukkanin fasinjoji 149 da da ma’aikatan kamfanin jiragen sama Habasha guda 8 dake kan hanyar su ta zuwa Nairobi babban birnin ƙasar Kenya suka mutu.
Hukumar da kula da sufurin jiragen sama ta ƙasar (ECAA) tace ta dage wa kamfanin haramcin gudanar da ayyuka ne bayan ta gamsu da cigaba da kamfanonin ya samu a bangaren kira jiragen sa, da kuma horas da matuka jirgin.
Tun A watan Nuwambar shekarar 2020 Hukumar sufurin jiragen sama ta kasar Amurka (FAA) ta amince wa kamfanin da ya koma zirga-zirga, to amma bisa sharadin sake horar da matuka jirajen da sauya na’ urorin tashin jirgin wato Flights computer.