Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hadaddiyar Daular Larabawa ta karbi bakuncin taron komitin hadin gwiwa na UAE da Najeriya a karon farko a lokacin da bangarorin biyu suka tattauna kan hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki, inda suka bayyana muhimmancin kafa sabbin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Taron wanda ya gudana a ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa a Abu Dhabi.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/rashin-tsaro-majalissar-kasa-ba-zata-iya-tsige-buhari-ba-fadar-shugaban-kasa/
Ministan harkokin wajen kasar Sheikh Shakhboot bin Nahyan bin Mubarak Al Nahyan ne suka jagoranci taron tare da Ambasada Zubairu Dada karamin ministan harkokin wajen Najeriya.
Manyan jami’an gwamnatin Najeriya da dama ne suka halarci taron, kuma tawagar Masarautar ta hada da manyan jami’ai da ke wakiltar hukumomin tarayya da na kananan hukumomi daban-daban, kansnan kungiyoyi, da kamfanoni masu zaman kansu.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki, inda suka bayyana muhimmancin kafa sabbin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Har ila yau, sun tattauna damar yin hadin gwiwa a fannonin ciniki da tattalin arziki, SMEs, kasuwanci, makamashi mai tsafta, fasaha, ilimi, tsaro, hada-hadar kudi da banki, al’adu, matasa da wasanni, da sufurin jiragen sama.
Sheikh Shakhboot ya yaba da yadda kwamatin hadin gwiwa ke da shi wajen inganta hadin gwiwa tsakanin Masarautar da na Najeriya masu zaman kansu da na gwamnati tare da karfafa gwiwar mahalarta taron da su ci gaba da yin amfani da wannan dandali.
A nasa bangaren, Zubairu Dada ya bayyana aniyar Najeriya na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
An kammala taron komitin hadin gwiwa inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, ciki har da yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin al’adu da matasa da kuma yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin wasanni.