Kungiyoyin lafiya na hadin gwiwa (JOHESU) da Majalisar Kwararrun Ma’aikatan Kiwon Lafiya sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 15, inda suka ce za su fara yajin aiki sai baba ta gani kan manyan matsalolin na walwala dake addabar ‘ya’yan kungiyar.
Mista Biobelemonye Josiah, Shugaban JOHESU na kasa, shi ne ya bayyana hakan a cikin wasikar da ya aike wa Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige, da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Asabar a Abuja.
Josiah ya ce wa’adin kwanaki 15 din ya biyo bayan kula da nuna halin ko in kula da gwamnati ke yi kan membobinta.
A cewar Josiah, lamarin walwalarsu ya haɗa da daidaita Tsarin Albashin Kiwon Lafiya (CONHES) kamar yadda aka yi tare da Tsarin Albashin Likitoci (CONMESS) tun daga 2014, tare da biyan duk wanda aka hana albashinsu daga watan Afrilu da Mayun 2018 na membobinsu, da kuma biyan albashin da aka rike a Asibitin Gwamnatin Tarayya na Owerri, JUTH da LUTH, bitar rashin aiwatar da alawus na yaki da cutar COVID-19, aiwatar da shawarar Kotun Ma’aikatu ta Ƙasa (NICN) na ‘Alternative Dispute Resolution (ADR), bin hukuncin kotu da sauran hukuncin kotuna, ƙara yawan shekarun ritaya daga shekaru 60 zuwa 65 ga ma’aikatan kiwon lafiya da kuma zuwa shekaru 70 ga Kwararrun ma’aikatan Lafiya.
”Sauran kuma sun hada da biyan alawus na haɗarin da aka fuskanta wanda zai ba da tabbacin yin gaskiya da adalci ga duk waɗanda abin ya shafa, biyan ainihin kashi 30 na ayyukan hadari da aka fuskanta domin ƙarfafa gwiwa na sauya canjin aiki ga ma’aikatan jinya/ungozoma da sauran su.
“Biyan alawus na koyarwa ga membobi dake kan CONHESS 7 da 8 (Ma’aikatan lafiya, Unguwanzoma da sauran su) da kuma sanya wadanda suka kammala karatun aikin jinya da masu koyan aikin a kyakkyawan tsari” in ji shi.
Ya jaddada cewa; “ku kasance cikin shirin tafiya yajin aiki idan kun gwamnati ta cije wajen kin biya mana bukatunmu”, ya lurantar da su.
Josiah, ya tabbatar da cewa kungiyarsu ta JOHESU ta nuna Dattako, rashin son kai da kishin ƙasa duk da matsanancin halin matsi da takurawa da gwamnati ta yi musu na hana su hakkokinsu.