By Ishaq Dabai
Rundunar tabbatar da bin doka da oda ta jihar Ogun TRACE ta tabbatar da mutuwar wata mata a hatsarin motar daya afku tsakanin babbar mota da babur a Iyana-Cele akan babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta.
Kwamandan Rundunar Owode-Ijako na TRACE, Misis Temitope Oseni, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Asabar a Ota, Ogun, tace wani namiji ya samu raunuka daban daban.
Oseni ta bayyana cewa hatsarin, wanda ya faru da misalin karfe 1.50 na rana, ya shafi wani babur dan kasuwa mai lamba GBE 476 WU da wata babbar mota Iveco, mai lamba KRD 43 XE.Ta kara da cewa mai babur din wanda ke kan gudu, yana kokarin wuce wani abin hawa a wurin da aka karkatar da shi lokacin da ya yi karo da babbar motar dake tafiya.
Oseni tace mutane hudu, wadanda suka hada da maza uku da mace guda, sun yi hadari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar matar yayin da namiji daya ya samu rauni.sannan taa kara da cewa wanda abin ya rutsa da shi daya daga cikin fasinjojin babur din ya mutu nan take.
Tace, “gawar wanda ya mutun ‘yan sanda sun tafi da ita, inda suka mika ta ga’ yan uwansa, yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba don yi masa magani,” in ji ta.
Kwamandan sashin ya bayyana cewa an ja motar da babur zuwa ofishin ‘yan sanda na Ifo, don saukaka zirga zirgar ababen hawa a yankin.Kazalika Ta shawarci masu babur na kasuwanci dasu guji yawan wuce gona da iri da tukin ganganci da kan iya haddasa asarar rayuka a kan hanyoyi.