Rundunar tsaro ta Civil Defence reshen jihar Ondo, ta bayyana cewa akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mutane 19 suka samu munanan raunuka a wani hadarin kwale -kwale a jihar.
Hukumar ta ce hatsarin ya afku ne a wurare daban -daban a karamar hukumar Ilaje da Irele na jihar a kwana kwanan nan.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar , Mista Olufemi Omole ya fitar a a jiya Lahadi, a Akure, babban birnin jihar.
Kwamandan rundunar na jihar, Dakta Hameed Abodunrin, a cikin sanarwar ya nuna damuwar sa kan halin ko -in -kula da matafiya ke nuna, yana mai cewa, wadanda abin ya rutsa da su sun mutu ne a cikin hatsarin saboda gaza sanya rigar kariya wato Live Jaket.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindigan Da su kayi Garkuwa da Daliban Jami’ar Lafiya sun bukaci Milliyan 20
Ya bayyana cewa rundunar a shirye take ta cafke masu kwale -kwale ko fasinjojin da suke saba dokokin tsaro kan amfani da ruwa wajan tafiye tafiye.
Kazalika Kwamandan jihar ya kara bayyana cewa, an tura jami’an hukumar zuwa ” Karamar Hukumar Irele don aikin ceto wadanda lamarin ya shafa, yayin da aka samu gawar mutum biyu da hadarin jirgin ruwa ya rutsa da su, Wadanda aka bayayna sunan su kamar haka; Oki Michael da Omogbehin Adebayo.” Inji sanarwar.