A ranar Lahadin da ta gabata ne mutane uku suka mutu yayin da daya ya samu rauni a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Legas zuwa Ibadan.
Hatsarin ya afku ne a kewayen Ogere gaban gadar Saapade a karamar hukumar Remo ta Arewa.
Jami’ar ilimin jama’a na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta.
A cewar ta, hatsarin ya rutsa da wata babbar mota kirar Mack mai lamba SMK 499 XU da kuma mota kirar Nissan mai lamba GH 598 LND.
A wani lamari mai ban takaici, wata uwa da yaronta Sunday sun kone “ba za a iya gane su ba” a lokacin da wata tanka mai dauke da man fetur ta fashe a Abeokuta, jihar Ogun.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babbar kasuwar Lafenwa da ke babban birnin jihar.
An kuma bayyana cewa, motar dakon man ta kife ne da misalin karfe 04:45 na safe, yayin da take kan hanyarta ta Oju zuwa Irin, da ke unguwar Lafenwa a Abeokuta, inda ta zubar da abinda ke cikinta a kan titin.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) dake jihar Ahmed Umar ya tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta.