• Hadarin ya afku ne a jiya juma’a da daddare.
• Mutun talatin ne hadarin ya rutsa dasu a cikin motoci biyun da su ka yi taho mugama.
• Hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin.
Hukumar kiyaye hadari ta kasa reshen jihar Osun, a yau Asabar, ta tabbatar da mutuwar mutun 11, daga cikin Wandada hadari ya rutsa dasu a Gbangan, na babban hanyar Badun.
Jami’ar wayar da kan al’uma na shiyar Mrs Agnes Ogungbemi ce, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa data fitar kuma ta rabawa mane labarai a Osogbo.
Ogungbemi ta ce hadarin ya afku ne da misalin karfe 9 da minti 21 na daren jiya juma’a, inda tace, lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ayedaade, mai nisan kilo mita 5 daga Gadar Sasa na jihar.
Ta ce ” Wata motar mai dauke da lamba KJA392YA wacce fara Mazda E200 ce, da wata Bakar Toyota Kirar Hiace, mai dauke da Lamba GWL427YM ne,su kayi taho mugama da juna” Inji ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake a jihar Ekiti.
Ta ce “Mutanan da hadarin ya rutsa da su, sun kai talatin, inda akwai mata biyu da karamar yarinya daya” inji jami’ar.
Inda takaran da cewa, a nan take ne, mutun 11 suka mutu, 22 suka sami mummunan raunikan, Kuma akayi gaggawar kai su asibiti domin duba lafiyar su.
Comments 1