Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) ta ce mutane biyu sun mutu a wani hatsarin mota a ranar Lahadin nan, yayin da wata motar bas kirar Toyota Hiace ta daki wata babbar motar da ke tsaye kusa da Annex CID na ‘yan sanda da ke kan titin Onitsha-Awka.
Wannan lamarin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar FRSC ta Anambra, Mrs Margaret Onabe ta fitar ranar Lahadin nan.
A cewar sanarwar, hatsarin ya rutsa da wata babbar mota mai lamba FKJ 22 da wata mota kirar Toyota Hiace mai lamba GDD 68 ZP, da misalin karfe 8:45 na dare.
“Wataƙila abin da ya haifar da hatsarin shine toshewar hanya da kuma gudun wuce sa’a.
“A cewar wani wanda ya shaida lamarin, motar ta samu matsala kuma direban motar ya ajiyeta bayan ya sanya alamun kariya a gaba da bayan motar.
“Direban bas din da ke cikin sauri ya daki bayan motar ya yin hadarin,” in ji sanarwar FRSC.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/ku-kai-hari-dazuzzuka-da-tsofaffin-kangwaye-igp-ga-jimian-yan-sanda/
Ta ce yayin da mutane 12 da suka hada da maza takwas da mata hudu suka hatsarinbya ritsa da su, biyu sun mutu, biyar kuma suka samu raunuka daban-daban.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Onabe ta bayyana cewa, jami’an hukumar FRSC Nteje wadanda suka kai daukin farko sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti tare da ajiye wadanda suka mutu a dakin ajiye gawarwaki na New Word Mortuary a garin.
Sanarwar ta ce, Kwamandan sashin Anambra na hukumar FRSC, Adeoye Irelewuyi, ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.
Ya ce rundunar ta gargadi masu ababen hawa da su daina yin gudu da kuma kiyaye ka’idojin da aka gimdaya musu.
(NAN)