• Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Ekiti ya tabbatar da afkuwar lamarin.
• Mutun bakwai aka tabbatar da mutuwar su a hadarin da ya afku da sanyin safiyar yau Talata.
• Kwamishinan yan sandan jihar ya jajantawa iyalan mamatan da lamarin ya rutsa da su.
Jami’an yan sandan sun tabbatar da mutuwar mutun 7, inda wasu kuma su ka sami raunuka, a wani hadarin mota da ya afku a hanyar Iluomoba zuwa Aisegba, dake Karamar hukumar Gbonyin na jihar Ekiti.
Jaridar Independent ta ruwaito cewa, hadarin ya afku ne da wata motar bas kirar Luxurious, mai dauke da lamba: BDG-47-WT da kuma wata motar bas kirar Hummer mai lamba: ABC-82-XH.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Sunday Abutu ya fita, ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 6 na safe yau Talata, ya yin da motocin biyu su kayi taho mugama da junan su.
Sanarwar ta ce, “Tawagar jami’an yan sandan, karkashin jagorancin DPOn yankin, da wasu jami’an hukumar kare haddura ta kasa, sun isa wajan da lamarin ya faru cikin gaggawa, inda su ka kwashe wadanda suka sami raunuka n zuwa asibitin koyar wa na jami’ar jihar Ekiti da ke Ado-Ekiti” inji sanarwar.
Kazalika sanarwar tace, Kwamishinan yan sandan jihar Ekiti, Tunde Mobayo da mataimakin gwamnan jihar Chief Egbeyemi, sun ziyarci wurin da lamarin ya afku.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nasarorin Sanata Uba Sani cikin shekara biyu
Inda Kwamishinan, ya jajantawa iyalan mamatan, da kuma fatan Allah ya jikan su baki daya.
Ya kuma yi wa wadanda ke asibiti, domin cigaba da duba lafiyar su, fatan samun lafiya cikin sauki.
Comments 1