Hadimar Buhari Onochie ta musanta batun cewa Tinubu bai da Takardun makaranta
Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa akan Kafafen Sadarwa na Zamani Laurette Onochie ta musanta batun da ke yawo cewa Bola Tinubu Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC bashi da takardu.
Onochie ta bayyana labarin cewa Tinubu bashi da takardar Firamare da Sakandare a matsayin Karya ne.
A cikin wani saƙo data wallafa a shafin ta na Facebook, ta bayyana irin yadda aka yi ta yaɗawa cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bashi da ilmi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikar Shekaru 60: Ka cigaba da yiwa Najeriya aiki – Buhari ga Gbajabiamila
Ta alaƙanta wannan zarge-zarge akan Tinubu da waɗanda ke neman yakin zaɓe ga wasu Ƴan Takara.
Wasu rahotonni sun nuna cewa Tinubu ya sanar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC cewa an sace takardun shi a lokacin mulkin soji.
Tinubu yayi nuni dacewar ya karbi takardun shi akan shaidar kammala karatu na kasuwanci da Mulki a Jami’ar Chicago.
Da wannan batu, wasu ƴan Najeriya sun cigaba da tofa albarkacin cewa Tinubu baije makaranta ba.
Da take maida jawabi, Onochie ta rubuta “Mun ji su, bana tabbacin komi ya sanya basu iya kirkirar wata karya sai wannan.
“A 2014, Janar na Soji daya ajiye aiki, Muhammadu Buhari aka ce baije makaranta ba. Yanzu saura kasa da shekara ya kammala wa’adin sa na biyu a matsayin Shugaban Ƙasar mu.