Hadimin Wani Gwamna yayi kira ga Matasa dasu kula da Abokanan da suke tarayya dasu
Mai Taimakawa Gwamna Ifeanyi Okowa na Musamman akan Cigaban Matasa Mr. Buchi Omenogor yayi kira ga Matasa dasu zama masu kula akan abokanan da suke yawo su, domin gudun kada su jefa su a halin lalacewa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ɗan Acaɓa ya mutu a hannun Ƴan Sanda a Ogun bayan yasha Azabtarwa a hannun su
Omenogor ya bada shawarar a lokacin da yake rarraba kayayyakin Miliyoyin Nairori ga Al’ummar Amai a Ƙaramar Hukumar Ukwuani ta Jahar Delta.
Yace “Matasa sune ƙashin bayan kowacce Ƙasa, a saboda haka ina kira a gareku daku zama masu kula da Abokanan da zaku yi tarayya dasu, domin abinda kuke yi ko kuma tsunduma kan ku shine abinda zai baku dama zama Shuwagabannin gobe.
” Na yanke shawarar fara wannan aikin domin bani damar samar da ayyuka ga Matasa. Kuma lamarin shine goyon bayan Gwamna, wanda ya ƙirƙiri ayyuka da dama domin cire Matasa daga yawo akan Titi.”
A lokacin da yake kira ga Al’ummar dasu yi Kyakkyawan amfani da Kayayyakin, yace wani dalilin bada kayayyakin shine baiwa Matasa damar zama masu dogaro da kawunan su, tare da bada gudunmawa domin cigaban Jaha da Ƙasa baki ɗaya.
Yace lamarin dake sanya shi farin ciki shine yanda Matasa suka miƙa rayuwar su ga Mahallin cin su.
Comments 1