By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce hadin kai da hakuri su ne muhimman dabi’un da ake bukata domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’ummar addinai daban-daban kamar Najeriya.
DUBA WANNAN LABARIN: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Jami’in Kwastam Da Wasu Mutane 9 A Jihar Kaduna
Kakakin Osinbajo, Laolu Akande, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar limamai da malaman addinin Islama da shugabannin musulmi daga ko’ina a fadin kasar a Abuja.
Tawagar malamai sama da 25 da malamai da shuwagabannin kungiyoyi daban-daban sun fito ne daga manyan cibiyoyi da majalisar malamai ta kasa da kungiyar Qadiriyya da Fitiyanul Islam ta Najeriya da kuma Darika.
Haka kuma a cikin tawagar akwai Majalisar Matasan Musulmi ta kasa, Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya, Jammat Tajdidul Islamy, Kungiyar Matasan Salafiyya, Limamai na Masallatan Kasa da na Majalisun Dokoki na Apo, Abuja da dai sauransu.
Tawagar ta samu jagorancin Farfesa Siraj Abdulkarim daga jami’ar ABU Zaria, shugaban kungiyar ci gaban al’umma da ci gaban matasa na kasa (CYD), kungiyar malamai ta al’umma.
Da yake jawabi ga tawagar, Osinbajo ya ce har sai mutum ya yi hulda da jama’a ba zai iya bayyana abin da su da sauran su ke so ba.
Tun da farko, daya daga cikin shugabannin tawagar, babban limamin majalisar dokokin jihar Legas, Dakta Abdul Hakeem Abdul-Lateef, ya bayyana mataimakin shugaban kasar a matsayin shugaba mai kaunar daukacin ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ba.
NAN