Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce hadin kai, tsaro da ci gaban kasar ne yafi damunsa, sama da kasancewarsa lamba daya a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Buhari, wanda ya bayyana jin dadinsa da cewa jam’iyyar tana kan gaba, ya gode wa tawagar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
“saboda irin kalaman da na yi a kan rawar da na taka wajen zaben dan takararmu, da abokin takararsa, a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu, shekara mai zuwa.
‘’Ina so in gode muku da irin rawar da kuka taka wajen ginawa, da farko a babban taronmu na kasa a farkon wannan shekara, daga baya kuma, a zaben fidda gwani.
‘’Dukkanku masu tunani daya ne, kuna son abin da ya dace ga Jam’iyyar, kuma yan takarar an tabbatar da su bisa gaskiya da adalci.
‘’A gare mu baki daya, hadin kai da hadin kan Jam’iyyar shi ne abin da muka sanya a gaba.
Buhari ya tuna cewa a lokacin da aka gabatar masa da abokin takarar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, kwanaki biyu da suka gabata, ya ce zai ajiye ra’ayinsa har zuwa lokacin da za a yi bikin mika mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, a dandalin Eagle Square.
Shugaban, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shettima ba zai baiwa jam’iyyar kunya ba, da ma ‘yan Najeriya baki daya.
Ya kuma yabawa jam’iyyar kan matakin da ta dauka na kara hada kan ‘yan Najeriya musamman matasa domin yin rajista, da kuma karbar katin zabe na dindindin (PVCs).