Baban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya tabbatar wa yan Najeriya cewa rundunar soji najeriya na dukkanin mai yiwuwa wajen tinkarar harkar tsaro dake addabar kasar nan.
Irabo ya bada wannan tabbaci ne a yayin wani taron wuni guda na runduanr tsaro da ya gudana a babban birninj taryayya AbujA.
Ya ce jami’an sojin Kasar nan na ci gaba da damara na ganin sun maido da tsaro a fadin kasar nan da aikin ta’addanci ya daidaita.
Hafsan soji ya kara da cewa taron zai tattauana kan dukkannin matsalolin tsaro da masu ruwa da tsaki da ma duk wani da zai iya bada gudnumawar shi wajen dawo harkar tsaro a kasar nan.
A cewar shi matsalar tsaron kasar nan ya zama ruwan dare da ya fi karfin a tsaya ana ririrta ta, musamman matsalolin nan na Ta’addanci, fadar manoma da makiyaya, da matsalar fadace-fadacen addini da kabilanci da ma harkar garkuwa da mutane da yan fashin daji da suka zama ruwan dare.
Ya akra da cewa matsalolin tsaro a kasar ya daidata komai inda har ya kai ga kimar kasar ta wargaje a idanun duniya.