Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya amince da mayar da Naira 50,000 ga kowane mutum 1,318 a jihar da suka yi aikin Hajjin shekarar 2022.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwamishinan yada labarai Malam Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za Mu Ci Tarar Duk Kamfanin Jirgin Saman Da Ke Saida Tikitin Da Dala— FG
Ya bayyana cewa hakan na daga cikin matakan bayar da agajin da gwamnatin jihar ke yi domin rage wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.
Ya bayyana cewa hukumar alhazan ta tsara fara mayar da kudaden ne daga ranar 12 ga watan Satumba a kowace karamar hukuma 14 na jihar domin tabbatar da bin umarnin gwamna cikin gaggawa.
“Saboda haka, an shawarci alhazai da su je kananan hukumominsu inda suka biya kudinsu domin karbar Naira 50,000, daga ranar 12 ga Satumba,” ya kara da cewa.
Dosara ya kuma bayyana cewa Matawalle ya bada tabbacin kudirin gwamnati na inganta tsaro, samar da ababen more rayuwa da sauran ribar dimokuradiyya ga al’umma.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da marawa manufofinta da shirye-shiryenta goyon baya domin samun damar sauke nauyin da aka dora mata. (NAN).
A WANI LABARIN KUMA: Tinubu Ya Taya Sabuwar Firaministar Burtaniya Murna
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya taya sabuwar Firaministan Birtaniya, Liz Truss murna, tare da bayyana daukakarta a matsayin wani tsarin mika mulki cikin lumana.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar a ranar Laraba.