Rahotanni da suka fito daga Abujan, sun nuna cewa; daga cikin wadanda suka samu halartar zaman daga bangaren masu ruwa da tsakin ta fuskancin hajji sun hada da; kamfanukan dake jigilar alhazai, maniyyata hajjin, da kuma masu lura da tashi zuwa aikin hajjin.
Wani Otel mai suna Zamzam Pullman dake garin Makkah da Madina, ya gana da masu ruwa da tsaki ta fuskancin ayyukan Hajji a Nijeriya. Ganawar ta gudana ne a Abuja a ranar Talata domin ganin sun ba da wadansu kyautuka da tallafi domin ayyukan Hajji da Umrah.
Hameed Sidine, Babban Manajan rukunin Otel din, ya ce ziyarar zuwa Nijeriya domin bayar da wannan tallafin sun yi shi ne domin tallafawa mahajjatan Nijeriya domin su rika tunawa da aikin Hajjin da suka yi.
Har wala yau ya bayyana cewa; Nijeriya tana da dimbin Musulmai fiye da kowa yammacin Afrika, manufarmu shi ne mu tabbatar Hajjinsu da Umrah da suka yi ya zame musu abin tunawa. Otel dinmu mun yi su a wurare masu muhimmanci dake kusa da Makkah da Madina, wanda zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukan Hajjinsu da Umrah.
Ayman Ekayssouni, Daraktan huldar siyarwa da kasuwanci, ya ce yana da gayar muhimmanci rukunin kamfanin na su ya kawo ziyara Nijeriya, idan aka yi lura da yadda Nijeriya take da dimbin Musulmai masu aikin Hajji a duk shekara. Ya tabbatar da cewa; kamfanin na su yana da wuraren kwana da zirga-zirga masu kyawu ga mahajjatan Nijeriya, ya ce shiyasa suka zo domin kasance cikin wadanda za su tallafawa mahajjatan Nijeriyar.
A karshe sun tabbatar da cewa Otel din Zamzam Pullman a Makkah yana da dakuna 1, 315, da wuraren taruka, sannan wanda yake Madina yana da dakuna 836 da wuraren shirya taruka.