Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Ambasada Mohammad Abba Danbatta ya yi cikakken nazari kan al’amuran da suka kai ga gazawar aikin Hajjin da ya gabata a fadin kasar nan.
Dambatta ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da SOLACEBASE, a Kano, inda ya ce manyan abubuwan da suka haifar da rashin aikin a cikin atisayen da ya gabata, sun hada da jinkirin shirye-shiryen da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi da kuma takaita guraben da hukumomin Saudiyya suka baiwa Najeriya zuwa 43000 kacal.
KU KARANTA KUMA NAHCON Da Saudiyya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Aikin Hajjin Bana
A cewarsa, hakan ya faru ne a lokacin da jiha kamar Kano ta riga ta sami koma baya na aƙalla maniyyata 2500, daga kalandar aikin Hajji da aka soke a shekarar 2020 da 2021 sakamakon annobar COVID-19.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Danbatta ya kara da cewa a shekarar da ta gabata an rage rabon kujerun da jihar ta samu zuwa 2229, wanda hakan ya sa jihar ta samu babban gibi.
Sakataren zartarwa na hukumar alhazai ta jihar, ya kuma yi tir da yadda hukumar NAHCON ke gudanar da wasu munanan manufofin da ke kara ta’azzara matsalar da ake fama da ita na yadda ake tafiyar da dimbin alhazai a jihar.
‘’Daga cikin wadannan tsare-tsare, a cewarsa, har da saka wani jirgin da ba shi da karfin tafiyar da jigilar fasinjoji, duk kuwa da turjiya daga gwamnatin jihar Kano da hukumar alhazai ta jihar.
Dambatta ya kara da kakkausar suka ga shugabancin hukumar alhazai ta Kasa kan takaita gwajin COVID-19 ga dukkan maniyyatan jihar zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke Kano, duk kuwa da cewa jihar na da sauran cibiyoyin kiwon lafiya masu inganci da babban asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Ya kuma kara da cewa, a atisayen da aka yi a baya an amince da hukumar ta buga biza sama da dubu uku a kullum amma shugabancin NAHCON na yanzu ya takaita bugawa da bayar da takardar tafiye-tafiye zuwa shedikwatar hukumar da ke Abuja, lamarin da ya sanya ta sami rauni.
Sai dai ya bayyana fatansa cewa da shirye-shiryen farko na bana da kuma karin guraben da aka ware wa Najeriya, ayyukan Hajjin bana za su samu nasara sosai.
Ya kuma bayyana cewa za a fara duba maniyyatan da aka yi watsi da su a aikin hajjin bara, sai kuma wadanda suka biya a kan lokaci, inda ya ce tuni hukumar ta fara karbar kudi naira miliyan 1.5 daga hannun maniyyata.
A cewar Danbatta, tuni hukumar alhazai ta jihar ta samu takardar izini daga gwamnatin jihar Kano domin fara shirye-shiryen gudanar da atisayen na bana.
A Wani Labarin Kuma Gwamnatin Legas Ta Bada Wani Umarni Ga Gidajen Sayar Da Man Fetur
Gwamnatin jihar Legas ta umurci dukkan manyan masu sayar da man fetur masu zaman kansu da ke aiki a kan manyan tituna a jihar da su bude tsakanin karfe 9 na safe zuwa 4 na yamma a ranakun mako.
Gwamnati ta yi gargadin duk wani ma’aikacin da ya ki bin umarnin daga yanzu za a saka masa takunkumi mai tsanani.