Hukumar jin dadin Alhazai ta Kasa NAHCOH, ta ce za a fara tantance kamfanonin jiragen saman da zasu gudanar da jigilar mahajjata aikin Hajjin 2023 a makon farko na watan Maris.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Shugaba kuma Babban Jami’in Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da manema labarai ranar Talata a Abuja.
Hassan ya ce makasudin zaman tattaunawa da ‘yan jarida shi ne a kara fahimtar juna da kwararrun kafafen yada labarai.
KU KARANTA KUMA NAHCON Za Ta Fara Karbar Kudin Aikin Hajji A Wata Gobe
Ya ce hukumar na aiki tukuru don ganin an gudanar da aikin Hajjin 2023 lami lafiya domin alhazan Najeriya su samu damar gudanar da aikin hajjin karbabbe.
Hassan ya ce: “Kuna sane da cewa an baiwa hukumar NAHCON kujeru 95,000 kuma dole ne in gaya muku cewa mun je Masarautar Saudiyya ne domin ziyarar aikin Hajji na farko da muka yi domin sanin masu aiki da kuma tantance masu hidima.
”Mun riga mun ware wuraren aikin Hajji ga Jihohin Tarayya 36 da Babban Birnin Tarayya da kuma Rundunar Soji.
“Muna kan aiwatar da wasu abubuwa da yawa bayan haka za mu sami wata hanyar sadarwa ta zamani.
”Muna da niyyar fara tantance kamfanonin jiragen sama nan da makon farko na watan Maris. Ina mai tabbatar muku da cewa aikin hajjin bana zai samu inganci.
A cikin sakon sa na fatan alheri, kwamishinan ayyuka na NAHCON, Alhaji Abdullahi Magaji-Hardawa, ya ce hukumar ta kudiri aniyar ganin ta biya bukatun alhazan Najeriya na aikin hajjin bana.
Ya ce shugabancin hukumar a kodayaushe a bude take wajen bayar da shawarwari da kuma shirye-shiryen amsa tambayoyi daga manema labarai a matsayin amintattun abokan aikin hukumar. (NAN)/Solacebace
A Wani Labarin Kuma Tsagin G5 A Jam’iyyar PDP Za Su Yi Aiki A Ranar Zaben Shugaban Kasa — Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce tawagar tsakin G5 ta jam’iyyar PDP ba ta kare ba, ya kara da cewa tsagin zai aiwatar da shirinsa a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a lokacin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar a karamar hukumar Ahoada ta Gabas.