Tsohon Shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya ce, da a ce Yesu Al-masihu na Nijeriya a wannan lokacin, ba zai iya kauda kai daga lamuran da ke faruwa a kasar ba.
Jaridar Punch ta ruwaito tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na cocin Foursquare Gospel Church a Nijeriya karo na 64, wanda aka gudanar a jihar Ogun.
Obasanjo ya ce ganin halin da kasar ke ciki, ya kamata Malaman addinai su rika fitowa suna magana kan abubuwan da suka addabi kasar, kamar yadda jaridar ta Punch ta ruwaito.
Punch ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya bukaci babban Malamin cocin da ya kai cocin mataki na gaba sannan sai ya yi hanzarin karawa da “Ban fa ce ka kai ta ‘next level’ ba.”
Obasanjo dai na shagube ne ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan takenta na “next level.”