Kwamishinan Ƴan Sandan Jahar Enugu Abubakar Lawal a ranar Talata ya umarci dukkanin manya dake ƙarƙashin rundunar da suka haɗa da shuwaganni na yankuna da Ƙananan Hukumomi dake yankin Al’ummomin Nkanu ta Gabas, da Nkanu ta Yamma, da Al’ummomi a Enugu ta Kudu inda Gwamnatin Jahar ta hana zirga-zirgar Babur mai taya uku da Okada, da manyan Motoci da su tabbatar anbi dokar.
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi a ranar Juma’a, bayan taron gaggawa da Masu ruwa da tsaki a Ƙananan Hukumomi guda biyar a Enugu ta Gabas, ya sanya doka dake hana zirga-zirgar Adaidaita, da Babur mai Ƙafa biyu da Manyan Motoci a Yankunan.
Hana zirga-zirgar tuni ya haifar da yin Allah wadai daga Shuwagabannin Majami’u ciki harda Rabaran Fr Ejike Mbaka, Wanda ya bayyana sanya dokar a matsayin rashin bin Shawara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin ta sake zama teburin tattaunawa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU
Mbaka yace dalilan da Gwamnati ta bayar na sanya dokar, kwata-kwata basu da ma’ana.
A dai lokacin da Gwamna Ugwuanyi yake taro da Shuwagabannin Manyan Motoci Tipper dana Adaidaita, da Okada, Kwamishinan Ƴan Sandan ya Umarci jami’an shi, dasu tabbatar da an bi dokar a dukkanin Al’ummomin da lamarin ya shafa.
Kwamishinan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Mai sa Hannun Mai Magana da Yawun Rundunar Daniel Ndukwe a ranar Talata, wanda ya sanar dashi ga wakilin Majiyar mu.