Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a jiya ya yi Allah wadai da kisan da Tanko Abdulmalik, mallakin makarantar Noble Kids, ya yi wa wata daliba Hanifa Abubakar, inda ya ce gwamnatin tarayya na son a yi adalci.
Abdulmalik ya amsa laifin kashe Hanifa, ‘yar shekara biyar dalibar makarantar, wadda aka ce an sace ta a watan Disamba, kuma masu garkuwa da su sun bukaci a biya su Naira Milliyan 6 a matsayin kudin fansa kafin sakin ta.
Ya ce ya kashe dalibar da “gubar bera”, kuma ya binne gawarta a harabar makarantar tare da taimakon wani abokinsa.
A wata sanarwa da ministan ya fitar a jiya, ya ce lamarin cin zarafi ne ga daukacin aikin koyarwa, kuma bai kamata a bari ya sake faruwa ba, ko da a nan gaba.
Ya ce: “Muna sa ido sosai kan wannan bala’i da ya faru a Kano, kuma muna sha’awar ganin cewa ba kawai a yi adalci ba, a’a a bayyane za a yi shi.
“Idan yaro ba zai iya tsira a hannun malaminsa ba, Toh ina kuma yaron zai iya tsira?”
Adamu ya yaba da matakan da gwamnatin jihar ke dauka na shawo kan lamarin.
Yayin da ya jajanta wa iyayen dalibar, ministan ya yi addu’ar Allah ya jikan ta ya Kuma Bayarwa da Iyayena mafificin alheri.