Kungiyar Kano Leadership Enlightenment and Advocacy for Development Initiative (Kano LEADS) ta ce za ta tabbatar da an yi adalci wajen kisan da aka yi wa wata daliba Hanifa Abubakar da Tanko Abdulmalik, mallakin makarantar Noble Kids ya yi.
Tuni dai Abdulmalik ya amsa laifin kashe Hanifa, ‘yar shekara biyar dalibar makarantar, wacce aka ce an sace ta a watan Disamba, kuma masu garkuwa da ita suka bukaci a biya su Naira Milliyan 6.
A jiya kungiyar ta bukaci gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, da ya tabbatar da aiwatar da duk wani mataki da kotu ta yanke kan kisan Hanifa.
Da take jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, shugabar kungiyar LEADS ta Kano, Hajiya A’isha I. Dankani, ta ce: “Ya kamata Abdulmalik Tanko ya kasance amintaccen malaminta (Hanifa).
“Lokaci ne da al’umma za su sake tunani. Doka ta fito karara a irin wannan yanayi inda wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
“Gwamnatin jihar Kano da hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa sun nuna sha’awarsu kan lamarin, ciki har da hukumomin da abin ya shafa. Dole ne kowa ya nuna himma wajen tabbatar da an yi adalci,” in ji Dankani.
Ta ce dole ne a wayar da kan iyaye kan muhimmancin ilimin zamani.
“Su (iyaye) suna buƙatar saka hannun jari a cikinsa, daidai da darajar da suke ba wa Islamiyya da karatun Alqur’ani.” Inji ta.