Daga Sulaiman Musa
An dakatar da zirga-zirgan fasinjoji a babban hanyar Enugu Abakaliki biyo bayan jin karar harbe-harbe da wasu ‘yan bindiga dadi suka yi a kan babban hanyar Ezilo.
Babu wani bayanin kan wadanda suka kaddamar da wannan harbe-harben.
Majiyarmu ta ruwaito cewa an kashe mutane biyu a wani sabon rikicin kan iyaka tsakanin al’ummar Exilic da kuma garin Iyionu da ke makwabtaka da su.
Dukkanin kauyukan suna cikin karamar hukumar Ishielu a jihar ne.
Sai dai ba a iya danganta harbe-harben da aka jiyo da wannan lamarin ba.
Wani matafiyi daga Afam Cyprian, wanda ke hanyarsa daga Enugu, ya bayyana cewar fasinjoji da dama sun kasance a warware a Okpoto na tsawon awanni.
Jami’ar watsa labaran ‘yan sandan jihar, Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin harbe-harben.
Ta bayyana cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarcin tura jami’an ‘yan sanda domin tabbatar da maido da doka da oda a yankin.