A masana’antar Bollywood ta ƙasar India akwai jaruman da idan suka shigo cikinta sukan yi sa’a suyi saurin kafa kansu wato su shahara da wuri, hakan baya faruwa sai dai idan fim ɗinsu na farko ya samu karɓuwa a lokacin daya fito aka fara haska shi a gidanjen kallon fina-finai na India wato sinimu kenan wanda idan akayi sa’a wani fim ɗin a cikin ‘yan kwanaki ake mayar da kuɗinsa.
Daga haka kuma idan aka ga jarumi yayi kasuwa manyan masu bayar da umarni zasuyi ta saka shi a cikin fina-finansu daga nan duniya zata sake saninsa sosai da sosai inda cikin ‘yan shekaru zai fara lashe manyan kyaututtuka da dukkanin wani abu daya danganci Bollywood, inda jarumai da dama hakan ta faru a kansu angani.
Sai dai akwai wasu jaruman maza da mata suna fuskantar matsala idan har fim ɗinsu na farko baisamu karbuwa ba inda kuma daga nan tauraruwarsu take disashewa, idan hakan ta faru kuma koda wani daraktanne zai sakaki ko zai sakaka a fim sai kawai kaga an sauya sunan wani ya maye gurbinka ko ya maye gurbinki a wanda ko wacce zata fito a cikin fim ɗin.
Hakan ya faru da jarumai da dama a masana’antar ta Bollywood kuma hakan suka haƙura suka rungumi ƙaddara sunaji suna kallo ba a fiye kiransu ba domin ayi fim dasu inda koda a watannin da suka gabata akwai jarumar datayi wannan kukan na irin wannan ƙaddarar data afkamata.
Idan mun dawo maganar da jarumi Suchin yayi ta cewar hanya ɗaya ce tak jarumi ko jaruma ka iya kafa kansu itace duk wanda ya san zaiyi fim to ya tabbata labarin cikin fim ɗin ingatacce ne wato labari ne mai kyau, domin idan kasan bashi da kyau ko ma anarsa bazata gamsar da al’umma ba to babu makawa jarumi zai sami kansa a ruwa tsumu-tsumu domin hakan ya faru da wasu da dama.
Jarumin ya ƙara da cewa sananan yana shawartar jarumai idan zasuyi fim sudinga yi sunajin kamar da gaske ne kamar yadda yakeji a zuciyarsa idan yana yin fim, haka zalika yayi kira da jarumai akan idan zasu dinga yin amfani da labari mara kyau domin yin fim to matsala bazata ƙaremasa ba.
Har yanzu matasa naci gaba da tasowa a masana’antar ta Bollywood kuma masu baiwa inda kuma ana ganin a nan gaba zasu bayar da gudun mawa sosai da sosai wato kuma jaruman gasu nan maza da mata, sai dai wasu daga cikin ‘ya’yan jaruman akan sami albasa batai halin ruwa ba inda wasunsu abubuwan da sukeyi daban.
Shidai Sachin ya fara fim tun a shekarar 1990 kuma har yanzu yanayin fim, daga cikin fina-finan da yayi daga 1990 zuwa yanzu akwai Pal pal dilke paas da Friendship Unlimited da Luramba da Lover da Jeeva Sakha da Ziddi da Bichhoo da sauransu.
Sai dai a halin yanzu a masana’antar dai an sami ɓullar wasu abubuwa da ake ta cece-kuce akai wato jaruman da ake ta zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi wato abin da ba’a saba gani ba a duniyar masana’antar ta Bollywood dake can ƙasar ta India, danagane da hakan dai mutane da dama musamman tsofaffin jaruman na India maza da mata da sukayi Allah wadai da wannan wuta data kunno kai a masana’antar ta Bollywood.
Ana nan ana taci gaba da bincike ka’in da na’in akan wannan al’amari kuma har yanzu sababbin fuskoki naci gaba da bayyana akan zargin ta’ammali da amfani da miyagun ƙwayoyin inda tabbas kuma akwai alamun za a ɗauki tsatsauran mataki akan al’amarin.