Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Babban bankin kasa CBN ya bude shafin da al’umma zasu ziyartan, domin cike wasu ka’idoji da nufin kai tsohon kudin su zuwa banki.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da bankin, ya jaddada cewa ba zai sake karbar tsofaffin kudi ba daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Ministocin sa
Ga yadda tsarin kai kudin ka zuwa CBN yake.
Da farko zaka shiga wannan link din
Www.crs.cbn.gov.ng akan wayar ka, bayan ka tabbatar kana da Kyakkyawar hanyar sadarwa.
Daga nan zai kai ka zuwa mai shafi na daban da zai tambaye ka taba ajiye kudin ta wannan tsari ko sabon mai ajiya ne, sai ka taba saboda idan kai sabo ne.
Daga nan zai sake kai ka wani shafin na daban kamar haka:
Customer BVN *
Enter BVN
BVN Name *
BVN Name
BVN Phone *
BVN Phone
BVN Email Address *
Bank *
Select Bank
Account Number *
Enter your account number
Account Name *
Account Name
Depositor Phone Number *
Enter phone number
Depositor Email Address *
Enter email address
Depositor Address *
Enter address
Amount of ₦200 Notes *
Enter amount
Amount of ₦500 Notes *
Enter amount
Amount of ₦1000 Notes *
Enter amount
Total Deposit *
Total Deposit
Wadannan bayan na sama duk zaka bi ka cike su ne daidai da yadda suka tambaye ke, a kasan kasa zaka ga wani koren waje sai ka taba, daga nan zaka samu wata lambar shaida da banki zasu sauraren ka idan kaje da tsohon kudi.
A haka har kudin su tabbatar da shiga asusun ka na ajiya.
A wani labarin kuma: Sam Emefele Bai Cancanci Zama Gwamnan CBN Ba – Inji Wani Gwamna
Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo, a ranar Laraba, ya bayyana cewa gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, bai cancanci shugabancin babban bankin ba.
A cewar Akeredolu, ya kamata a kori gwamnan CBN daga ofis lokacin da ya nuna sha’awar tsayawa takarar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.