Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shine wanda ya san hanyar samarwa da talakawan Najeriya sauƙi.
Ƙoƙari, himma, juriya, jajircewa gami da sanin makamar shugabanci irin na mai girma ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu, su ne su ka haifarwa ƴan Nageriya wasu muhimman nasarori.
A dalilin ƙoƙarin ɗan takarar na APC, ƴan Najeriya sun samu sauƙi kan matsalolin da sauyin kuɗaɗe suka haifar.
KU KARANTA KUMA: Matashi ya samu sauyin rayuwa bayan ya taki sa’ar yin wuff da wata kyakkyawar baturiya
Ga wasu daga cikin ƙoƙarin da Tinubu yayi domin ganin ƴan Najeriya sun samu gagarumin sauƙi kan matsalar sauyin kuɗi.
1. Cigaba da karɓar tsofaffin kuɗaɗe da sabbi.
2. Dakatar da cirar cajin banki a kuɗin mutane.
3.Tabbatar da wadatar kuɗaɗe a banki.
4. Wayar da kawunan al’umma game da tsarin.
5. Samar da kwamitin magance matsalar ƙarancin kuɗaɗe.
6. Samar da tsarin daidaita ayyukan banki.
Wannan wata ƴar manuniya ce da ke ƙara tabbatarwa da ƴan Nageriya cewa Asiwaju ba barci ya ke ba, kullum cikin hidima ya ke domin ganin talakawan Nageriya sun samu sauƙin rayuwa.
Al’amura sun daidai an samu cigaba a yanzu kenan da ba ma shi ne shugaban ƙasar ba, balle kuma ace shi ne, ba shakka al’ummar Nageriya za su yi barci da idanuwan su ba a rufe ba tare da wata fargaba ba.
Zaɓen 2023: Bola Tinubu Shi Ne Mafitar ‘Yan Najeriya a Daidai Wànnan Lokaci
Lokacin da ya zama gwamnan Jihar Legas a shekarar 1999 Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya samu nasarar bunƙasa harajin Jihar daga Naira Miliyan 600 duk wata, zuwa Naira Biliyan 8.2 a shekarar 2007.
A daidai wannan lokacin da Nageriya ta ke cikin matsayin tattalin arziƙi, ta na buƙatar Asiwaju wanda ya ke da ƙwarewa da dabarun bunƙasa tattalin arziƙi domin samun mafita.