Wani dan asalin kasar Uganda dake zama a California, A.J Ssesanga ya ce bai taba ganin kyakkyawar mace ‘yar Najeriya ba, LIB ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, karkashin wata wallafa a Twitter wacce ake lissafo jerin kasashen Afirka masu kyawawan mata.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ce gonarsa ce kawai a ransa
A jerin an lissafo kasashen inda aka fara da kasar Ghana, Tanzania, Najeriya, Uganda, sannan Afirka ta Kudu.
Ganin hakan ne A.J ya yi gaggawar bukatar a cire Najeriya daga jerin kasashen saboda a cewarsa shi dai har yau bai gamu da kyakkyawar mace ba ‘yar Najeriya.
Ma’aikatar Aikin Gona Ta Jaddada Manufarta Ta Hada Kai Da Kafofin Yada Labarai
Babban sakataren ma’aikatar noma da raya karkara, Dr Ernest Umakhihe, ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da hada kai da kafafen yada labarai wajen gudanar da ayyukanta.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Umakhihe ya bayyana haka ne a wajen wani taron bita na yini daya da sashen yada labarai na kungiyar masu aiko da rahotannin aikin gona ta shirya a Abuja.