Sidi Aminu Sharif, daya daga cikin fasinjojin jirgin da suka samu ‘yanci bayan shafe sama da watanni hudu a tsare, ya bayyana halin da ya shiga.
Wanda aka sako din, kuma guda cikin fasinjoji biyar da aka sako ranar Talata, an harbe shi a yayin mamayar, lamarin da ya kara nuna damuwa game da yanayin lafiyarsa.
Da yake magana a ofishin Tukur Mamu na Kaduna, mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna, kuma wanda ya taimaka wajen sakin wasu fasinjojin jirgin, wanda abin ya shafa ya ce kokarin da aka yi na cire harsasan bai yi nasara ba.
DUBA WANNAN LABARIN: Daliban jami’ar Kaduna sun koma karatu
Ya bayyana fatansa na samun kulawar da ta dace yanzu da aka sallame shi.
“Ina daya daga cikin fasinjojin jirgin da aka kai wa hari akan jirgin Kaduna yayin da yake akan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna. Ina iya tuna yadda abin ya faru a lokacin da muka fara jiyo hayaniya da kururuwar jama’a.
Yayin da muke zaune a cikin jirgin, ina iya tunawa ina addu’a lokacin da muka ji ƙara mai ƙarfi, daga bisani sai harbe Harbe, kuma ina daga cikin wanda Harbin ya sama, duk da cewa Wani likita yayi kokarin cirewa amma ya kasa.
Ya yi amfani da tufafina don tsayar da jinin da ke fita daga wajen da Harbin ya shiga.”
“Ya yi amfani da safar hannu ya bincika cikina ya ciro harsashin amma bai samu ba, daga baya ya yi amfani da almakashi amma har yanzu bai samu ko da harsashi a cikina ba, kuma har zuwa yanzu, ba mu ga harsashi ba. Ban sani ba ko har yanzu yana cikin jikina, ina fatan yanzu da muka samu ’yanci, zan iya zuwa asibiti a duba hoton idan har an samu harsashin.” inji shi
Har yanzu dai ba a san ko an biya wani kudin fansa domin a sake su ba, amma Daily Trust ta rawaito yadda fasinjojin da aka sako a watan Yuli suka biya kowannen su Naira miliyan 100, yayin da dan kasar Pakistan din a cikinsu ya bayar da Naira miliyan 200 domin samun ‘yanci.
‘Yan ta’addan wadanda da farko suka bukaci a yi musanya da mutanan su dake a gidan yari a matsayin daya daga cikin sharuddan sakin fasinjojin, sun bukaci a biya su makudan kudin fansa bayan da shugabanninsu da suke so a yi musu musanya wadanda suka tsere a yayin harin gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje dake Abuja.