A jiya Litinin ne hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa har yanzu babu wata mafita da aka samu da zata dakile cutar sarƙe numfashi baki ɗaya.
Magunguna da dama suna kan gwaji a fuska ta uku kana muna sa ran za a samu magunguna masu inganci da zasu taimaka wurin kare mutane daga kamuwa da cutar. Koda yake har wa yau,b a samu mafita ba kuma tana yiwuwa ba za a samu ba, inji darektan hukumar lafiyar ta duniya Dakta Tedros Adhanom, ya bayyana hakan ne a jiya yayin wata ganawarsa da manema labarai.
Adhanom ya yi kira ga ƙasashe da ɗaiɗaikun mutane kowa ya bada taimakon da zai iya wurin gwaji da bibiyar masu cutar da nesanta da juna da kuma amfani da takunkumin hanci, da ma dukkanin wasu matakan kare kai.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da kamuwa da cutar da mace mace daga COVID-19 ke kara yaɗuwa a fadin duniya. Ya zuwa jiya Litinin, an tabbatar da mutum miliyan 18 da dubu ɗari biyu ne suka kamu da cutar, a cewar hukumar nazarin Korona da jami’ar John Hopkins, lamarin da ya kai wadanda suka mutu a dalilin cutar zuwa dubu 691 da dari uku.