Yayin da ake shirin fara rubuta jarabawar kammala sakandire ta yammacin afurka (WAEC) a ranar 16 ga watan mayun da muke ciki zuwa 23 ga watan Yuni a kasar nan.
Makarantun gwamnati a jihohin Sokoto da Zamfara basu mikawa hukumar dake shirya jarabawar sunan koda dalibi daya da zai rubuta jarabawar ba.
Shugaban hukumar a kasar nan Patrick Areghan, ya bayyana haka a Litinin din nan a Lagos yayin da yake bayyana irin shirin da sukayi na rubuta jarabawar.
Ya ce makarantu masu zaman kansu ne kawai sukayiwa dalibai rijistar rubuta jarabawar inda yace basu da masaniya kan dalilin da yasa makarantun gwamnati basu bada sunayen daliban da zasu rubuta jarabawar ba.
Dalibai miliyan daya da dubu dari shida ne sukayi rijistar rubuta jarabawar ta WAEC daga makarantu dubu ashirin da dari biyu da ashirin da daya a kasar nan.