Har yanzu akwai yan matan makarantar Chibok 88 dake tsare wajen masu garkuwa da su, wato yan ta’addan Boko Haram.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Adadin Yan Matana da Boko Haram suke sace ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, sun kasance 276, kuma sauran wasu sun tsira wasu kuma sun mutu.
Shugabar tawagar hadin gwiwa a yankin Arewa Maso Gabas, Colonel Obinna Ezuipke ne ya tabbatar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ahelkwatar rundunar dake Maimalari a Birnin Maiduguri.
KARANTA ANAN: Sarauniya Elizabeth II Ta Taimaki Najeriya Lokacin Yaƙin Basasa – Buhari
Ya kara da cewa daga cikin 276 da aka sace, 57 sun kubuta tun a shekarar, yayin da 107 suka kubuta a shekarar 2018, 3 a 2019, yayin da 2021, biyu suka ku ta daga hannun yan ta’addan.
Sauran da suka kubuta sun haɗar da 9 a shekarar 2022, kuma idan aka hada yanzu haka 178 suka kubuta daga cikin 276, wanda hakan ya sa yanzu akwai ragowar 98 a hannun yan Boko Haram din.
Ya ce jami’an su zasu ci gaba da kai farmaki zuwa maboyar yan ta’addan, don ganin sun fatattakesu, tare da kuɓuta da sauran yan matan.
A wani Labarin Kuma: PDP Ta Sake Rasa Wani Jigo Bayan Ya Kara Mai Zuwa Jam’iyyar APC
Tsohon sanata kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar Yobe Alh. Adamu Garba Talba, ya sake ficewa daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan dai na zuwa ne watanni biyu bayan da Sanata Talba ya koma PDP daga APC.