Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce alkawuran da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, bai cika su ba. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Ologbondiyan, wanda ya yi magana a cikin wani shiri na gidan talabijin Channels TV Mai suna “Sunrise Daily” ya ce abin dariya ne a yi maganar inganta tattalin arzikin Najeriya a karkashin wannan gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Kori Wani Dan Takarar Gwamna A APC
Ya ce, “Manyan alkawurra guda uku da Buhari ya yi alkawarin su a lokacin yakin neman zabesa, duk bai cika su ba. Yanayin yaki da cin hanci da rashawa ko yaki da tada kayar baya da inganta tattalin arzikin kasa, babu wanda Buhari ya cimma a cikin wadannan kudurorin.
“A karkashin gwamnatin APC cin hanci da rashawa yasamu wurin zama. Dole ne in fadi hakan a fili kuma ’yan Najeriya sun sani, a tarihin kasar nan, ba mu taba ganin cin hanci da rashawa ba kamar yadda muke gani a yau.”
Ologbondiyan ya kalubalanci duk wani dan jam’iyyar APC da ya fito kan titunan kasar nan ya ce Buhari ya taka rawar gani a jagorancinsa.
Ya kara da cewa, “Jeka Kasuwar Area Daya (a Abuja) ko Kasuwar Oyingbo da ke Legas ka ce, su ne abubuwa mafi alherin da Buhari yayi a Najeriya.”
“Kun gaza ta kowane fanni, kun yi alkawarin samar da tsaro da ba ku samar da shi ba, kun yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa ba ku yi ba, kuma fannin tattalin arzikin shi ne abu mafi muni, a ganina me za ku zo ku fadawa ‘yan Najeriya?”
A WANI LABARIN KUMA: Sarki Charles III Ya Ketare Zuwa Scotland Jim Kadan Da Binne Mahaifiyarsa
Sarkin Biritaniya, Sarki Charles III ya tashi zuwa Scotland washegarin bikin jana’izar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Ya bar filin jirgin saman Aberdeen a yau Talata bayan ya tashi daga RAF Northolt a yammacin London.