By Abbas Yakubu Yaura
Tuni dai wakilan taron jam’iyyar APC na kasa suka hallara a dandalin Eagle Square dake Abuja, suna jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
DUBA WANNAN LABARIN: Akalla Sojoji 25 Sun Shiga Cikin Mawuyacin Hali Bayan Afkuwar Wani Hatsarin Hanya
Zuwan shugaba Buhari zai kasance a hukumance a fara gudanar da taron wanda ake sa ran zai samar da sabon kwamitin ayyuka na kasa (NWC).
Ana kuma sa ran taron zai amince da kuma aiwatar da sabon kundin tsarin mulkin jam’iyyar tare da zaben shugabannin zartarwa na shiyya.
Kamar yadda shirin taron da aka fitar ranar Juma’a ya nuna cewa Buhari zai isa wajen da karfe 3:15 na rana. Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto bai iso ba.
Wakilan da za su halarci babban taron su ne: Gwamnoni masu ci, tsofaffin gwamnoni, Sanatoci, shugabannin jihohi, shugabannin kananan hukumomi, ’yan majalisar dokokin jiha, ’yan majalisar wakilai da dai sauransu.
Wasu daga cikin jiga-jigan VIP da wakilai da suka isa wurin taron sun hada da Sakataren Kwamitin Tsare Tsare-Tsare na Jam’iyyar APC Sanata John Akpankudohede; Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun; Yahaya Bello na jihar Kogi; Abdullahi Sule na jihar Nasarawa; Abubakar Sani Bello na jihar Neja; Kayode Fayemi na Ekiti.
Sauran sun hada da ministocin harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio; Labarai da Al’adu, Lai Mohammed; tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Borno, Kanar Abdulmumin Aminu mai ritaya; tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode; Sen. Ita Enang; Abike Dabiri-Erewa; da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim.
Comments 1