Shugaban Jam’iyyar APC a jihar Bayelsa Dennis Otiotio, ya ce tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan har yanzu ba dan Jam’iyyar su bane a jihar.
Dennis ya bayyana hakan ne yayin Wata ganawa da aka yi da shi ta wayar tarihi, a safiyar yau Alhamis.
Ya kara da cewa Jonathan zai iya zamadan jam’iyyar ne idan har ya tabatarwar da duniya hakan, kuma aka samu shugaban Jam’iyyar na kasa Adamu Abdullahi shima ya tabbatar da hakan.
Otiotio na wannan jawabi ne dai dai lokaci da labarin cewa Jonathan ya koma APC ke ci gaba da zagaye Najeriya, wanda a cewar sa hakan ba gaskiya bane.
To sai dai ya ce suna maraba da kudirin Jonathan din, idan har ya kai ga yanke shawarar Komawa jam’iyya mai mulki.
Har yanzu dai ana ci gaba da cece kuce kan gaskiyar komawar Goodluck Jonathan jami’iyyar APC.