Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce har yanzu yana da kyakkyawan alaka tsakaninsa da gwamna Ganduje da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Shekarau wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, shi ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da ‘yan jarida a yau Lahadi a Kano.
A cewarsa Shekaru, babu wani sabani a tsakaninsa da Ganduje da kuma Kwankwaso da sauran wadansu ‘yan siyasa a Kano.