Daya daga cikin ‘yan matan da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su wadda aka ceto kwanan nan, Jinka Yama, ta ce har yanzu tana son haduwa da mijinta na Boko Haram inda ta dage cewa har yanzu tana sonsa.
Gatekeeper News ya tattaro cewa, Yama na son mijin nata ya ajiye makamansa ya mika wuya ga sojojin Najeriya domin burinta na sake haduwa da shi ya zama gaskiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Ta Maka Gwamna Abdulrazaq A Kotu Bisa Zarginsa Da Yin Amfani Da Jabun Takardu
Yama ta shaidawa manema labarai a hedikwatar Operation Hadin Kai (OPHK) cewa har yanzu tana kewar mijin ta na uku, Usman wanda shi ne mahaifin ‘ya’yan biyu daga cikin ‘ya’yanta uku.
Ta ce ta gaya wa mijinta manufarta ta tserewa, sai ya ce mata ta aikata burinta na ganin ta kubuta.
A wani labarin kuma, Kasar China Ta Bude Ofishin ‘Yan Sanda A Najeriya
Gwamnatin kasar Sin ta bude ofisoshin ‘yan sanda a Najeriya da kuma a wasu saran kasashe sama da 20 na Turai da Amurka da Asiya da Afirka a kokarin da take yi na magance yawaitar laifukan ‘yan kasar a kasashen waje.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa ta bincike mai taken, ”’Yan sandan shiga tsakani 110 na kasar Sin a kasashen waje sun tafi daji.’